banner

002

001

google-site-verification: googlee60b5eec5b8450ce.html

Arewa mufarka

Koton daukaka Kara takori Goodwill akpabio a matsayin Dan takarar sanata a apc

 Akpabio

Sa'a 1 da ta wuce

Kotun daukaka kara  da ke Abuja  ta  yi watsi da  hukuncin da wata babbar kotun tarayya a birnin ta yanke inda ta cire Godswill Akpabio a matsayin dan takarar jam'iyyar APC na mazabar Akwa Ibom ta Arewa maso yamma a Majalisar Dattijai.

Hukuncin kotun wanda alkalai uku suka yanke da mai shari''a Danlami Senchi  ya karanta a ranar Litinin  ya ce Akpabio ya gaza gabatar da shaida a cikin lokacin da doka ta tanada.

Alkalan sun kuma ce, kasancewar Akpabio, dan takarar shugaban kasa a Jam'iyyar APC, ba zai iya shiga sahihin zaben fidda gwani na jam'iyyar da aka gudanar a  ranar 27 a watan Mayu ba wanda aka yi a gaban jami'an hukumar zabe mai zaman kanta inda aka gabatar da Udom Ekpoudom a matsayin dan takarar jam'iyyar.

A hukuncin da wata babbar kotun tarraya  da ke Abuja  ta yanke a ranar 22 ga watan Satumba ta nemi hukumar ta INEC ta mayar da Sanata Akpabio a matsayin dan takarar jam'iyyar ta APC, a matsayin dan takarar da ta tsayar a zaben fid-da-gwani karo na biyu  da aka yi a ranar 9 ga watan Yuni.

No comments:

Post a Comment